Ba mu biya kuɗin fansa wajen sakin waɗanda aka yi garkuwa da su ba – Gwamnati

0
113

Gwamnatin Nijeriya ta ce ba ta biya wani kuɗin fansa ba wajen ganin an sako mutanen da aka yi garkuwa da su a harin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna na ranar 28 ga Maris.

Ministan Sufuri na ƙasa, Mua’zu Sambo, a cikin wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai ya ce “ba a biya ko da sisin kobo ba na kudin fansar sako mutane 23 da aka yi garkuwa da su da sauran su.”

Jaridar The Nation ta rawaito cewa da ga nan, Sambo ya sanar da cewa bayan sako wadanda lamarin ya rutsa da su, ana shirin ci gaba da gudanar da zirga-zirgar jiragen kasa batareda jinkiri ba.

“Domin dawo da ayyukan jirgin kasa, dole ne mu samar da matakan da za su tabbatar da cigaba da irin wannan lamari dan ganin hakan bai sake faruwa a kasar nan ba.

Dangane da dalilin da ya sa wadanda abin ya shafa ba su halarci taron ba, ministan ya ce suna bukatar kulawa da lafiya da kuma wasu hanyoyin da ake bukata bayan ceto su.

Daganan Ministan ya bayyana cewa bayan ganawar da shugaban kasa ya yi da wadanda akayi garkuwa da su a ranar Juma’a, tuni aka sada su da iyalansu.