Barau FC ta samu damar buga gasar Premier ta Najeriya

0
6

Kungiyar ƙwallon ƙafa ta Barau FC ta samu nasarar samun gurbin shiga Gasar Premier League ta Najeriya (NPFL) bayan da ta lallasa Doma United da ci 2-0 a wasan da aka buga ranar Alhamis. Usman Maidubji da Shammasu Muhammad ne suka jefa ƙwallayen da suka tabbatar da nasarar.

Wannan shi ne karon farko a tarihin ƙungiyar da za ta taka leda a matakin mafi girma na ƙwallon ƙafa a ƙasar nan.

Wannan kuma ya share fagen gasar hamayya tsakanin Barau FC da Kano Pillars, duk daga jihar Kano, a kakar wasa mai zuwa, karo na farko da hakan zai faru a tarihin NPFL.

Barau FC ƙungiya ce da ke karkashin mallakar Sanata Barau Jibrin, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya.

A wani labarin makamancin haka, Wikki Tourists ta jihar Bauchi ma ta samu damar komawa gasar bayan shafe shekara guda a matakin ƙasa, tun bayan faduwarta daga Premier League a shekarar 2023.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here