Ƴan bindiga sun halaka mutane 13 Mariga dake jihar Neja

0
65

Akalla mutum 13 sun rasa rayukansu a wani hari da ƴan bindiga suka kai kauyen Mongoro da ke karamar hukumar Mariga a Jihar Neja. Cikin waɗanda suka mutu har da ɗan sanda ɗaya da ƴan sa-kai uku, kamar yadda rahotanni suka nuna.

Wani mazaunin Wamba wani gari da ke cikin Mariga ya shaida wa Daily Trust cewa har zuwa misalin ƙarfe 5 na yammacin ranar Laraba, maharan na ci gaba da addabar yankin.

Idan za’a iya tunawa ko a ranar 24 ga watan Yuni, wasu ƴan bindiga sun kai hari kan wata barikin sojoji da ke Kwanan-Dutse a Mariga, inda suka kashe sojoji 17 tare da jikkata wasu 10. 

Shugaban karamar hukumar Mariga, Abbas Adamu Kasuwan-Garba, ya tabbatar da faruwar lamarin, sai dai ya ce ba a tantance ainihin adadin waɗanda suka mutu ba, inda yace ana cikin zaman dar-dar a yankin sakamakon hare-haren da ke ci gaba da faruwa tsawon makonni.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, ya tabbatar da aukuwar harin, amma ya ce, basu kammala tattara bayanai akan harin ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here