Mai magana da yawun tsohon Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, Malam Garba Shehu, ya ce babu wata matsala ko rashin jituwa tsakanin Buhari da Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.
A wata hira da ya yi da BBC, Shehu ya bayyana hakan yayin kaddamar da littafinsa mai taken “According to the President”, inda ya bayyana darussan da ya koya daga aiki da Buhari.
Ya ce Buhari mutum ne mai kau da kai daga harkokin da ba su shafe shi kai tsaye ba, shi ya sa baya tsoma baki a al’amuran gwamnati yanzu.
Garba Shehu ya ce littafin yana bayani ne kan rayuwar Buhari da irin tsarin mulkinsa, domin gyara fahimtar da wasu ke da ita game da mulkinsa na shekaru takwas.
Ya ce akwai darussa da dama da matasa da ’yan jarida za su iya koya daga irin yadda gwamnatin Buhari ta gudanar da aiki, musamman a fannin tsaro, diflomasiyya da shugabanci.