Matsananciyar yunwa na damun miliyoyin ƙananun yaran arewa—Red Cross

0
11

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Red Cross ta Najeriya ta bayyana cewa fiye da yara miliyan 5.4 na fama da rashin abinci mai gina jiki a jihohi tara da rikice-rikicen tsaro suka shafa a Arewacin Najeriya.

A cewar hukumar, jihohin da lamarin ya fi shafa sun haɗa da Borno, Adamawa, Yobe, Sokoto, Katsina, Zamfara, Neja, Benue da Kano.

Shugaban rikon kwarya na sashen kula da lafiya na Red Cross, Dr. Aminu Abdullahi, ne ya bayyana hakan a lokacin ƙaddamar da shirin gaggawa na yaƙi da matsalar ƙarancin abinci mai gina jiki a yankin Arewa maso Yamma, wanda aka gudanar a jihar Kano ranar Talata.

Daga cikin adadin yara da abin ya shafa, kimanin miliyan 1.8 na fama da matsanancin rashin abinci mai gina jiki.

Dr. Abdullahi ya ce, kusan kashi 63 cikin 100 na kananan hukumomin waɗannan jihohi na cikin mawuyacin hali.

 Yace matsalolin tsaro sun tilasta mutane barin gonakinsu da gidajensu, lamarin da ya janyo karancin abinci. Ba wai yawan abinci kaɗai ba, har da rashin ingancinsa.

Ya ƙara da cewa Red Cross na aiki a matakin rigakafi ta hanyar haɗin gwiwa da al’umma, wayar da kai da kuma tantance yara masu fama da rashin abinci mai gina jiki don tura su wurin samun kulawa ta musamman.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here