Gwamnatin tarayya zata ƙara kuɗin wutar lantarki

0
13

Ministan Makamashi, Adebayo Adelabu, ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya na aiki kan sauya tsarin yadda ake ƙididdige farashin wutar lantarki zuwa tsarin da ya dace da gaskiyar kuɗin wutar lantarki da al’umma ke samu, domin dakile ƙarin bashin Naira tiriliyan 4 da kamfanonin lantarkin ke bin gwamnatin.

Adelabu ya bayyana hakan ne yayin taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a Abuja, inda ya ce wannan wani bangare ne na gyare-gyaren da gwamnati ke shiryawa domin farfaɗo da bangaren wutar lantarki, tare da tabbatar da dorewar sa da jawo hankalin masu hannun jari.

Koda yake gwamnati ta ƙara farashin wutar ga masu shan wuta a rukunin Band A, wanda jama’a na ci gaba da kokawa kan ƙarancin wuta da kuma biyan kuɗin gyaran kayayyakin da ba sa aiki yadda ya kamata.

Sai dai ministan ya ce wannan mataki yana da muhimmanci matuƙa wajen haɓaka tattalin arziki da cigaban ƙasa.

A cewar wasu rahotanni, daga watan Disamba 2024, kamfanonin lantarkin suna bin gwamnati bashin kimanin Naira tiriliyan 4, wanda ya samo asali ne daga tallafin wutar da ba a biya ba.

A wata hira da Daily Trust, shugaban sashin kare hakkin masu siyan kayayyaki,  Kunle Olubiyo, ya bayyana cewa ƙarin kuɗin wutar a halin yanzu na iya cutar da masu amfani da ita, ganin cewa ba a samun wutar yadda ya kamata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here