Gwamnatin Tarayyar Amurka ta sanar da sabon sauyi a tsarin bayar da biza ga ‘yan Najeriya, inda ta rage lokacin ingancin biza da kuma yawan damar shiga ƙasar ga yawancin masu neman bizar da ba na jami’an diflomasiyya ba.
Wannan sanarwa ta fito ne a ranar Talata daga ofishin jakadancin Amurka da ke Najeriya, inda aka bayyana cewa mafi yawan nau’ikan bizar da abin ya shafa za su kasance na shiga Amurka sau ɗaya kacal tare da wa’adin wata uku kacal.
Sabon tsarin zai fara aiki nan take, wanda ke nufin duk masu neman sabuwar biza za su samu biza da ke da tsawon kwanaki 90 ne kawai da damar shiga ƙasar sau ɗaya, sai dai waɗanda tsarin ya keɓe su, tun ba farko.