Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da fitar da ƙarin Naira biliyan 6 domin biyan haƙƙoƙin ma’aikatan gwamnati da suka yi ritaya da kuma iyalan ma’aikatan da suka rasu.
Mai bawa gwamna shawara kan harkokin yaɗa labarai, Ibrahim Adam, ne ya sanar da hakan a ranar Talata ta wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
A cewar Ibrahim, wannan ƙarin kuɗi na cikin kudaden da gwamnati ke biya na bashin Naira biliyan 21 da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya gada daga gwamnatin baya ta Dr. Abdullahi Umar Ganduje, wanda ya tara tsakanin shekarar 2016 zuwa 2023.
Ibrahim ya ƙara da cewa wannan shine karo na huɗu da gwamnan ke fitar da kuɗaɗen fansho tun bayan hawansa mulki a shekarar 2023.
Ya kuma ce bashin da Abba, ya gada gaba ɗaya ya kai Naira biliyan 48.6, amma gwamnatin yanzu ta biya Naira biliyan 27, daga cikin bashin.
Tsofaffin ma’aikata da iyalan waɗanda suka rasu sun dade suna kukan an barsu ba tare da kulawa ba, inda da dama suka bayyana cewa sun fada cikin talauci tun bayan barin aiki.
Sai dai har yanzu gwamnatin jihar ba ta bayyana adadin mutanen da za su ci gajiyar wannan sabon biya ba. Duk da haka, wasu majiyoyi daga hukumar kula da fansho sun shaida cewa ana sa ran fara biyan kudaden a cikin wannan mako.