NNPC ya bawa Gwamnatin tarayya Motoci 35 masu amfani da gas

0
7

Kamfanin mai na NNPC ya mika gudunmawar motocin haya 35 masu amfani da iskar gas (CNG) ga Shirin Shugaban Ƙasa na CNG (Pi-CNG), a wani bangare na goyon bayansa ga makamashi mai tsafta da arha.

A wajen bikin mika motocin da aka gudanar a Abuja, Shugaban NNPC, Injiniya Bashir Ojulari, ya ce wannan mataki yana nufin tallafawa sauyin makamashi a ƙasa, tare da rage dogaro da fetur da dizel.

Karamin mnistan Albarkatun Man Fetur (Gas), Ekperikpe Ekpo, ya ce shirin zai taimaka wajen rage tsadar sufuri da ƙara walwala ga al’umma, bisa tsarin “Sabon Fata” na Shugaba Tinubu.

Shugabannin sassa daban-daban na NNPC sun tabbatar da cewa za su ci gaba da jagorantar bunkasa CNG da makamashi mai dorewa a Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here