Hukumar Kula da Harkokin Wutar Lantarki ta Ƙasa (NERC) ta bayyana cewa Najeriya ta tafka asarar Naira biliyan 536.4 a matsayin tallafin wutar lantarki a cikin zangon farko na shekarar 2025.
A cikin rahotonta na watanni ukun farko na shekarar 2025, NERC ta danganta wannan adadin da rashin saita farashin da ya dace da tsadar samar da wutar lantarki a tsakanin kamfanonin rarraba lantarki (DisCos).
NERC ta ƙara da cewa, daga zangon ƙarshe na 2024 zuwa zangon farko na 2025, nauyin tallafin da gwamnati ke ɗauka ya ƙaru da Naira biliyan 64.7 daga Naira 471.69 biliyan zuwa Naira biliyan 536.40.
An bayyana cewa hauhawar wannan tallafi ya faru sakamakon matakin gwamnatin tarayya na dakatar da karin kudin lantarki da ake biya, duk da cewa tsadar samar da wutar lantarki ta karu.
Tallafin dai, bisa ga bayani daga hukumar, ana amfani da shi ne wajen rage nauyin kuɗin da kamfanonin rarraba wuta (DisCos) ke biya ga Kamfanin Kasuwancin Wutar Lantarki na Najeriya (NBET), wanda ake kira “DisCo’s Remittance Obligation (DRO)”.