Gwamnatin jihar Borno ta tabbatar da mutuwar mutane tara da kuma raunata wasu hudu sakamakon wani hari da ‘yan ta’addan Boko Haram suka kai a garin Malam Fatori, dake karamar hukumar Abadam.
Kwamishinan harkokin kananan hukumomi da masarautu na jihar, Sugun Mai-Mele, ne ya bayyana hakan a lokacin da ya wakilci Gwamna Babagana Umara Zulum a ziyarar jaje da suka kai wa al’ummar da abin ya shafa.
Mai-Mele ya tabbatar wa mazauna yankin cewa gwamnati na daukar matakan da suka dace domin tabbatar da tsaro da kariya ga garin Malam Fatori.
Haka kuma, kwamishinan ya sanar da bayar da tallafin kuɗi ga iyalan da suka rasa ‘yan uwansu da kuma waɗanda suka jikkata.