Hatsarin mota yayi sanadiyar mutuwar mutane 21 a hanyar Kano zuwa Zariya

0
5

Hukumar Kiyaye Hadurra ta Ƙasa (FRSC) reshen jihar Kano, ta bayyana afkuwar wani mummunan hatsarin mota ya faru a safiyar yau Lahadi, 6 ga Yuli, 2025, da misalin ƙarfe 8:23 na safe a Kasuwar Dogo, Dakatsalle, da ke kan hanyar Zaria zuwa Kano.

Hatsarin ya haɗa ne da motocin biyu, babban motar kaya (DAF Trailer) mai lambar rajista GWL 422 ZE, da Toyota Hummer Bus mai lambar KMC 171 YM.

Binciken farko da tawagar FRSC ta gudanar ya nuna cewa hatsarin ya faru ne sakamakon rashin bin ka’ida ta hanyar da direban motar Toyota Hummer Bus ya aikata, wanda ya haddasa karo da motar tirelar. 

Hatsarin ya yi muni matuƙa wanda ya haifar da ƙonewar motocin baki daya.

Adadin mutanen da hatsarin ya rutsa da su ya kai 24, inda, mutane 21 suka rasu, sannan 3 kuma suka ji raunika iri-iri.

An kai gawarwakin waɗanda suka rasu zuwa dakin ajiye gawawwaki na Asibitin Nassarawa da ke Kano, yayin da aka mika waɗanda suka ji rauni zuwa Asibitin Gwamnati na Garun Malam don samun kulawar likita.

Kwamandan sashen FRSC na Kano, CC MB Bature, ya bayyana alhini matuƙa bisa wannan babban rashi, inda ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan waɗanda suka rasu, tare da fatan Allah ya ba waɗanda suka jikkata lafiya cikin gaggawa. 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here