Zirga-zirgar jirgin ƙasa zata dawo a tsakanin jihohin Kano da Neja—NRC

0
9

Hukumar Sufurin Jiragen Ƙasa ta Najeriya (NRC) ta tabbatar da cewa za a dawo da cikakkiyar jigilar jirgin ƙasa daga Kano zuwa Minna kafin ƙarshen watan Disamba na wannan shekara, a wani bangare na kokarin farfado da harkokin sufurin jirgin ƙasa.

Daraktan gudanarwa na hukumar, Dr Kayode Opeifa, ne ya bayyana hakan yayin wata ziyarar aiki da ya kai ofishin hukumar na shiyyar Arewa da ke Zariya.

 Ya ce wannan mataki zai taimaka wajen farfaɗo da harkokin kasuwanci da tattalin arzikin al’ummar jihohin dama ƙasa baki ɗaya.

“Da zarar an dawo da ayyukan jirgin ƙasan, zai sauƙaƙa tafiyar fasinjoji da kaya daga Kano zuwa Zariya, daga Zariya zuwa Kaduna, da kuma Kaduna zuwa Minna,” in ji shi.

Dr Opeifa ya ƙara da cewa hukumar za ta gyara kayan aikin da suka tsufa a shiyyar Arewa ta hanyar yin amfani da kuɗaɗen kasafin kuɗi na shekarar 2025.

A ƙarshe, ya ce hukumar na da shirin haɗin gwiwa da gwamnatocin jihohin Neja, Kano da Kaduna, domin farfaɗo da zirga-zirgar jiragen ƙasa a tsakanin Minna da Kaduna da kuma Kaduna zuwa Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here