Wasu mutane takwas sun rasa rayukansu, yayin da wasu da dama suka jikkata sakamakon mummunan haɗarin mota da ya faru a safiyar Lahadi a kan titin Mile 2 zuwa Badagry, kusa da tashar mota ta Atura, a jihar Legas.
Haɗarin ya haɗa da wata babbar motar haya kirar Mazda mai ɗaukar fasinja 16 da ke ɗauke da lamba KJA 811 YF da kuma wata babbar motar DAF mai lamba T1 4636 LA.
Shaidun gani da ido sun bayyana cewa haɗarin na iya zama sakamakon ganganci da rashin kula daga direban motar haya.
A halin yanzu, hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Legas (LASTMA) ta bayyana cewa ta fara bincike kan musabbabin wannan haɗari.
Babban Daraktan LASTMA, Olalekan Bakare-Oki, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa mutane takwas, ciki har da direban motar hayar da mai taimaka masa sun rasu nan take a wajen hadarin.