Wata majiya mai ƙarfi daga jam’iyyar ADC ta bayyana cewa akwai yiwuwar wasu gwamnoni biyar na jam’iyyar PDP su sauya sheƙa zuwa jam’iyyar.
Majiyar, wanda tsohon sanata ne daga jihar Katsina, ya ce, Gwamnonin PDP guda biyar sun ba mu tabbacin cewa za su shigo ADC. Sai dai suna jiran a ga ƙarshen fitinar Wike a cikin PDP. Muna sa ran haɗuwa da su bayan taron gangamin jam’iyyar na gaba domin nazari da yanke matsaya.
Ya ƙara da cewa wasu daga cikin gwamnoni, har da na jam’iyyar APC, na goyon bayan ƙungiyar hadakar data kafa ADC, tun watanni 18 da suka wuce muka fara shirya wannan haɗin gwiwar.
Wasu gwamnoni daga APC an tuntuɓe su kusan shekara guda da ta wuce. Sun amince da mu, amma ba zan bayyana sunayensu ba, inji majiyar.