Hisbah zata ɗaura auren yaran da suka ɗaurawa kansu aure babu sanin iyaye a Kano

0
9

Iyayen yaran da suka ɗaurawa kansu aure a Kano sun amince ayi Sabon biki karkashin koyarwar addinin Islama.

An samu wannan daidaito a lokacin da mahaifin Fatima, ya wakilta kwamandan Hisbah na Karamar Hukumar birni akan ya zama waliyyin amarya, bayan da al’ummar unguwar Yakasai da lamarin ya faru a yankin su suka biya sadaki Naira dubu dari da hamsin, zuwa ga asusun hukumar Hisbah da zata jagoranci daura auren.

Yusif Garba, shine ya jagoranci haɗa kuɗin sadakin don tallafawa yaran da suka yi wancan aure ba tare da sanin iyaye ba, yana mai cewa akwai bukatar tallafawa yaran.

Ustaz Hamidan Tanko Alasaka, shine babban kwamandan Hukumar Hisbah na karamar hukumar birni, yace an biya sadaki Dubu dari da hamsin kuma za’ayi wanan aure nan kusa.

Idan za’a iya tunawa dai Daily News 24 Hausa, ta kawo rahotan daura auren a unguwar Yakasai, tsakanin Aliyu da Fatima, ba tare da sanin iyayen su, wanda hakan ya haifar da ruɗani har iyayen amarya suka garzaya gaban Hisbah don neman ta raba auren.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here