Oluwatunbosun Awe, wani hadimi ga Sanata Olajide Ipinsagba mai wakiltar Mazabar Ondo ta Arewa, ya ajiye aikinsa sakamakon karancin albashin da yake karɓa na Naira 20,000 a kowane wata.
Awe wanda ke aiki a matsayin jami’in hulɗa da jama’a na gundumar Isowopo Ward 2 a Karamar Hukumar Akoko North East ta Jihar Ondo, ya sanar da murabus dinsa cikin wata wasika daya bayyanawa bainar jama’a ranar Laraba.
A cewarsa, wannan albashi ba ya da wata alaƙa da halin da tattalin arzikin Najeriya ke ciki a yanzu, balle kuma ya dace da sabon mafi ƙanƙantar albashi da gwamnatin tarayya ta amince da shi wanda ya kai Naira 70,000.
Ya ƙara da cewa, duk da cewa ya sha roƙon Sanata Ipinsagba da ya duba ƙara masa albashin, babu wani mataki da aka ɗauka.
Awe ya bayyana cewa ya yi aiki da Ipinsagba tun lokacin da ya ke mataimakin musamman kan harkar masana’antu a ƙarƙashin tsohon Gwamna Olusegun Agagu, inda har lokacin ma albashin da ya ke karɓa ya kasance Naira 20,000.
Da aka tuntubi mai magana da yawun Sanata Ipinsagba, Yinka Ajagunna, ya ƙi yin tsokaci kan lamarin.
Sai dai wani amintaccen Sanatan, Bankole Akerele, ya soki matakin Awe, yana mai cewa bai nuna godiya ba akan alkairin da ake yi masa.