Matasa sun daurawa kansu aure ba tare da sanin iyaye ba a jihar Kano

0
11

Wani mahaifi ya garzaya gaban Hukumar Hisbah ta Karamar Hukumar birni inda yake Neman daukinta kan cewar Wani matashi ya jagoranchin daura auren ƴarsa bada izininsa ba, a daren Laraba 2 ga watan Yuli 2025. 

Mahaifiyar Amarya Fiddausi Abubakar, tace tana Gida da daddare yara suka shigo gida inda suka bayyana mata cewa an daura auren yarta Fatima, hakan tasa hankalinta ya tashi kasancewar tasan ko kudin aure ba’a kaiwa yarta ba.

Mukhtar Musa Yakasai, shine mahaifin ango Aliyu, inda yace iyayen Amarya sun taba nemansu don sanar dasu cewa akwai soyyaya a tsakanin Aliyu da Fatima, sai dai a lokacin yace basu shirya yiwa ɗansu aure ba.

Ya ce kawai sai ji suka yi wai abokanan Aliyu sun daura masa aure, a ranar Laraba.

Aliyu Abdullahi, shine waliyin Amarya yace itace da kanta ta umarce shi ya daura Mata aure.

Usman Mahammmad, kuma shine wakilin ango yace shine ya jagoranci daura auren yana zaune aka gayyace shi da cewa zai yi wakilcin auren abokinsa.

Aliyu Mukhtar, wanda shine ango yace suna kaunar junansu kuma sune suka tsara yadda za’a daura auren. 

Fatima Amarya, itama tace tana kaunar ango, kuma an bata sadaki ta rike a hannunta, sannan ta roƙi kada a raba ta dashi.

Ustaz Hamidan Tanko Alasaka, shine babban kwamandan Hukumar hisbah na karamar hukumar birni yace wanan aure babu shi a shari’ar Musulunci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here