Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, ya bayyana cewa a shirye yake ya mara wa kowacce haɗakar jam’iyyun adawa da ke da niyyar kifar da gwamnatin APC a babban zaɓen shekarar 2027, amma ba tare da ya bar jam’iyyarsa ta PDP ba.
Lamido ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da jaridar Vanguard a birnin Abuja a ranar Laraba, inda ya nuna goyon bayansa ga haɗin gwiwar jam’iyyun adawa ƙarƙashin jagorancin tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata David Mark, karkashin jam’iyyar African Democratic Congress (ADC).
Sai dai tsohon Gwamnan ya bayyana cewa duk da goyon bayansa ga wannan yunkuri, ba zai fice daga jam’iyyar PDP ba, jam’iyyar da ya ce ya taka muhimmiyar rawa wajen kafa ta.
“Eh, a shirye nake da duk wani yunkuri na kifar da APC don a ceci Najeriya. Zan mara wa duk wanda ke da wannan buri. Zan shiga yaƙin neman zaɓe tare da su. Amma PDP ita ce jam’iyyata, kuma ba zan bar ta ba,” in ji Lamido.
Ya kara da cewa ba daidai ba ne a yi watsi da PDP saboda, a cewarsa, wasu “marasa godiya” na kokarin dagula lamuran cikin jam’iyyar.
“Ina da yakini da PDP. Ko da jam’iyyar tana fama da matsaloli a halin yanzu, zan zauna in yi gwagwarmaya don ceto ta,” in ji shi.