Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa lokacin da ya hau mulki a shekarar 2023, ya tarar da Najeriya cikin halin matsin tattalin arzikin da ta kusan rugujewa.
Tinubu ya bayyana hakan yayin wata ganawa da ‘yan Najeriya mazauna ƙasar Saint Lucia a birnin Castries ranar Laraba.
Ya jaddada cewa gwamnatinsa ta ɗauki wasu tsauraran matakai domin ceto tattalin arzikin ƙasar bayan karɓar mulkin.
Amma mun samu nasarar ceto tattalin arziki, Najeriya, wanda a yanzu yake farfaɗowa, in ji Shugaban.
Sai dai ya amince cewa talakawa basa samun kuɗi yadda ya kamata a karkashin jagorancin sa.