Masifar Tinubu tasa ƴan Najeriya neman Buhari ya dawo kan mulki—Ameachi

0
8

Tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, ya bayyana cewa halin rayuwa a Najeriya ƙarƙashin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ƙazanta matuƙa, har ta kai ga mutane na nuna sha’awar komowar tsohon Shugaba Muhammadu Buhari, kan mulki.

A yayin wata hira da manema labarai a birnin Abuja, Amaechi ya ce lamarin tattalin arzikin ƙasar ya tabarbare, inda hauhawar farashin kayayyaki da ƙarancin kuɗi suka jefa miliyoyin ‘yan ƙasa cikin ƙunci da yunwa.

Farashin abinci da sauran kayayyaki ya tashi fiye da kima, mutane ba za su iya siyan kayan da suke buƙata. Komai ya rushe,” in ji Amaechi.

Ya ƙara da cewa wahalhalun da ake ciki sun sa jama’a na dawowar mulkin Buhari.

Yanzu mutane na muradin Buhari ya dawo. A kullum, gwamnatin da ke zuwa tana yi wa mutane muni fiye da wadda ta gabata. Wannan ne yasa mutane ke ci gaba da tunanin gwamnatin baya,” in ji shi.

Amaechi ya bayyana cewa ya fice daga jam’iyyar APC a daren Talata, inda ya sanar da komawarsa jam’iyyar haɗaka ta ADC.

A kan dalilin da ya sa yake sukar gwamnatin da ya taɓa yi wa aiki, Amaechi ya ce matsalar Najeriya ba shugabanci kaɗai ba ne, illa tsarin mulki da siyasa gaba ɗaya, yana mai buƙatar sauyi na gaskiya.

Ya ce akwai buƙatar gina sabuwar tafiya ko tsari da zai haɗa al’ummar ƙasa domin ƙwato Najeriya daga hannun shugabanni marasa nagarta.

“Ni tun da fari ban taɓa ganin Tinubu a matsayin wanda ya dace ya shugabanci Najeriya ba,” in ji Amaechi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here