Lakurawa sun hallaka mutane da dama a jihar Sokoto

0
5

Rahotanni daga jihar Sokoto na bayyana cewa wasu da ake zargin mambobin ƙungiyar Lakurawa ne sun hallaka akalla mutane 15 a wani mummunan hari da suka kai ƙauyen Kwalajiya da ke ƙaramar hukumar Tangaza.

Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 2:00 na rana a ranar Talata, lokacin da maharan suka dira ƙauyen yayin da mazauna yankin ke cikin masallaci suna sallar Azahar.

Majiyar jaridar Daily Trust ta bayyana cewa harin na iya zama martani da mambobin ƙungiyar suka mayar bayan da  wasu daga cikin mayaƙan su rasu lokacin da suka kai wani harin da basu samu nasara ba.

Wani shugaban al’ummar yankin da ya nemi a ɓoye sunansa ya ce, suna cikin masallaci lokacin da aka kawo harin, sannan mayaƙan sun fara harbe-harbe ba bata lokaci.

Ya ƙara da cewa jami’an tsaro da shugaban ƙaramar hukumar Tangaza sun ziyarci ƙauyen a ranar Laraba domin halartar jana’izar waɗanda suka rasa rayukansu.

Wannan shi ne karo na farko da Lakurawa suka kai hari kai tsaye a garinmu. Amma ina ganin martani ne bayan kashe wasu daga cikin su a wani hari da ya faru a baya,” inji shi.

Wani mazaunin yankin ya bayyana cewa maharan sun ƙone gidaje da gonaki da dama, tare da lalata wata na’urar sadarwa da ke yankin, abin da ya bar al’ummar cikin tsananin fargaba da tashin hankali.


LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here