Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, ya bayyana cewa har yanzu yana nan daram a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), kuma bai da wani shiri na ficewa daga cikin jam’iyyar.
Shekarau, ya bayyana hakan a lokacin da yake karyata jita-jitar da ke yawo cewa ya koma jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), yana mai bayyana cewa labarin ba shi da tushe balle makama.
Sanarwar Shekarau na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da rade-radin cewa zai koma jam’iyyar ADC, musamman bayan da manyan shugabannin sabuwar haɗakar ‘yan adawa suka ayyana jam’iyyar ADC a matsayin wani dandalin da za su yi amfani da shi wajen fafatawa da Tinubu babban zaɓen 2027.