Babbar kotun jihar Kano da ke zaune a Miller Road, ƙarƙashin jagorancin mai shari’a Maryam Sabo, ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ga wani matashi mai suna Aminu Muhammad, bayan samunsa da laifin kashe yarinya ‘yar shekara uku mai suna Rafi’atu Junaidu.
Hukuncin ya fito ne a zaman kotun da aka gudanar ranar Laraba, 2 ga Yuli, 2025, inda mai gabatar da ƙara, Barista Badawiyya Shehu Bala, ta gabatar da shaidu uku. Sai dai lauyoyin da ke kare wanda ake tuhuma sun gabatar da hujja guda ɗaya kacal.
Kotun ta bayyana cewa ta gamsu da shaidun da masu gabatar da ƙara suka gabatar, don haka ta yanke hukuncin kisa ga Aminu Muhammad.
Lamarin ya faru ne tun a shekarar 2018, bayan da Aminu Muhammad ya ɗauki yarinyar daga gidansu zuwa wata gona da ke ƙauyen Jibga, cikin ƙaramar hukumar Bebeji. A nan ne ya shake ta, ya yanka cikinta da kwalba, sannan ya ciro kitsenta.
Rahotanni sun bayyana cewa wani ne ake zargin ya sa Aminu ya aikata wannan danyen aiki, inda ya yi masa tayin biyan Naira dubu ɗari huɗu (₦400,000).