Dakarun sojin Najeriya da ke aiki karkashin Operation Hadin Kai sun kai samame a maboyar ‘yan Boko Haram a yankin tafkin Chadi, inda suka kashe akalla ‘yan ta’adda 10 a wani artabu.
A cewar rundunar sojin, artabun ya faru ne a hanyar Rann zuwa Gamboru Ngala, kusa da iyakar Najeriya da Kamaru, inda ‘yan ta’addan suka dade suna gudanar da ayyukansu kafin su gamu da ajalinsu.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa hakan ya biyo bayan aikin haɗin gwiwa tsakanin dakarun Rundunar Hadin Gwiwa MNJTF, tare da haɗin guiwar Dakarun Haɗaka (Hybrid Forces) da sauran hukumomin tsaro.
A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, Daraktan Hulɗa da Jama’a na Rundunar Tsaro, Manjo-Janar Markus Kangye, ya bayyana cewa an gudanar da wannan samame ne domin kakkabe ragowar ‘yan Boko Haram da na ISWAP daga maboyarsu a yankin tafkin Chadi.
Manjo-Janar Kangye ya ce dakarun sun gudanar da aikin ne bisa sahihan bayanan sirri, inda suka mamaye mafakar ‘yan ta’addan a tsakanin Rann da Gamboru.