Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa Sanata David Mark, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar adawa ta PDP, yana mai cewa rikice-rikicen cikin gida da suka shafi shugabanci ne suka tilasta masa daukar wannan matakin. Kamar yadda Channels TV ta ruwaito.
Sanata Mark ya yanke shawarar barin jam’iyyar ne bayan kusan shekaru 27 da kasancewa a cikinta.
Sanata Mark, wanda ya shugabanci majalisar dattawa daga shekarar 2007 zuwa 2015, yanzu yana daga cikin jagororin sabuwar kawancen adawa da ke karkashin jam’iyyar ADC, wadda ke shirin ƙalubalantar gwamnatin APC a babban zaɓen 2027.
A cikin wata wasiƙa da ya aika wa shugaban PDP na mazaɓarsa ta Otukpo Ward a Jihar Binuwai, tsohon sanatan ya bayyana cewa jam’iyyar PDP ta rikice matuƙa, har ta koma abin dariya a idanun al’umma.
Na rubuta wannan wasiƙa ne domin sanar da kai a hukumance cewa na fice daga jam’iyyar PDP nan take,” in ji David Mark a cikin wasiƙar.
Rahotanni sun bayyana cewa David Mark na daga cikin ‘yan siyasar da suka kafa jam’iyyar PDP tun bayan kirkirowarta a shekarar 1998.
Ficewar Sanata Mark na zuwa ne a daidai lokacin da wasu fitattun ‘yan adawa ke ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa a ƙarƙashin jam’iyyar ADC domin fuskantar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027.