An Dakatar da Shugaban APC na Jihar Nasarawa Bisa Zargin Cin Amanar Jam’iyya

0
29

Shugabannin jam’iyyar APC a mazabar Gayam da ke Jihar Nasarawa sun dakatar da shugaban jam’iyyar na jiha, Alhaji Aliyu Bello, bisa zargin cin amanar jam’iyya.

A wata sanarwa da suka fitar, shugabannin mazabar sun bayyana cewa an dauki wannan mataki ne bisa zargin Alhaji Bello da aikata abubuwan da suka saba wa sashe na 21 na kundin tsarin mulkin jam’iyyar APC.

Sun ce halayen da shugaban jam’iyyar ya nuna sun nuna rashin biyayya da kuma yi wa jam’iyya zagon kasa, lamarin da ya sabawa ƙa’idojin tafiyar da jam’iyya mai mulki a jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here