Rundunar Civil Defence ta kama masu satat kayan gwamnati a jihar Kano

0
62

Rundunar tsaron a’lumma ta farin kaya Civil Defence  (NSCDC), reshen Jihar Kano, ta kama wasu mutum bakwai (7) da ake zargi da aikata laifin lalata kayan gwamnati da satar murfin ramin kwata guda goma (10) mallakin Hukumar Filayen Jiragen Sama ta Tarayya (FAAN) a Filin Jirgin Sama na Mallam Aminu Kano.

Wannan kame ya samu ne ta hanyar jami’an hukumar da aka tura don tsare wurin, inda suka mika wadanda ake zargin ga Sashen Yaki da Lalata Kayan Gwamnati na rundunar, wanda ya ci gaba da gudanar da bincike mai zurfi har ya kai ga kama wasu karin mutane da suka karɓi kayayyakin sata.

Sunayen wadanda ake zargin sun hada da:

Abubakar Umar, mai shekara 20

Sadiq Jafar, mai shekara 23

Iliya Nasir, mai shekara 20

Abba Muhammad, mai shekara 18

Al-ameen Idris, mai shekara 18

Haka kuma an kama wasu biyu da ake zargin suna karɓar kayan sata masu suna, Shamsu Ibrahim Usman, shekara mai 35, mazaunin Daiba Rijiyar Lemo, da Yusuf Abdulmumini, shekara mai 25, mazaunin Kurna Babban Layi

Kayan da aka kwato daga hannun wadanda ake zargi sun haɗa da murfin rami goma (10) da motar Mercedes Benz ɗaya (1).

A wani lamari mai nasaba da hakan, rundunar ta kuma kama wasu mutum biyu da ake zargi da laifin sata:

Haruna Musa, shekara 39, mazaunin Hotoro Kwanar Sabo, karamar hukumar Nassarawa

Sadiq Suleiman, shekara 27, mazaunin Rijiyar Lemo, karamar hukumar Ungoggo

Waɗanda ake zargin sun amsa laifin satar fitilun hasken rana guda huɗu (4) a kasuwar Kanawa da ke Dangwauro, karamar hukumar Kumbotso.

Dukkan mutunen za a gurfanar da su a kotu bayan kammala bincike, kamar yadda sashin shari’a na rundunar ya tanada, kamar yadda SC Ibrahim Idris Abdullahi, Jami’in hulɗa da jama’a, NSCDC, reshen Kano, ya sanar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here