Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa an ɗage jana’izar fitaccen ɗan kasuwa, Alhaji Aminu Dantata, wanda ya rasu ranar Asabar a Hadaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE), sakamakon wasu dalilai da suka shafi jinkirin isar da gawarsa zuwa birnin Madina, Saudiyya.
Ministan Yaɗa Labarai Mohammed Idris, ne ya tabbatar da hakan ga BBC, inda ya bayyana cewa gwamnatin Saudiyya na da ƙa’idoji masu tsauri dangane da shigar da gawa cikin ƙasarta domin gudanar da jana’iza, kuma ana ci gaba da shirin cike takardun da suka wajaba tsakanin iyalan mamacin da hukumomin Saudiyya.
“Ina tabbatar muku cewa an ɗage jana’izar Alhaji Aminu Dantata domin jiran cikakken izini daga hukumomin Saudiyya. Haka kuma, da zarar an kammala dukkan shirye-shiryen, za a ɗauko gawarsa daga UAE zuwa Saudiyya,” in ji Minista Idris.
Ya ƙara da cewa ofishin jakadancin Najeriya a Saudiyya tare da iyalan marigayin sun gama shirye-shiryen da suka dace domin gudanar da jana’izar.
Rahotanni sun nuna cewa Alhaji Aminu Dantata ya bar wasiyya da a binne shi a birnin Madina, inda iyalansa suka mika buƙatar hakan ga hukumomin Saudiyya, kuma an amince da ita.
A ranar Litinin da safiya ne tawagogin gwamnatin tarayya da ta jihar Kano suka tashi zuwa Saudiyya domin halartar jana’izar da aka shirya gudanarwa a yau.