Gwamnan Kano Ya Kaddamar da Rabon Takin Zamani Ga Manoma

0
21

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya kaddamar da rabon takin zamani ga manoman jihar a kan ragin farashi da ya kai kashi 50 cikin 100.

A cewar wata sanarwa da gwamnan ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Lahadi, rabon takin zai shafi dukkanin ƙananan hukumomi 44 na jihar.

Gwamna Abba ya bayyana cewa an ware tirela uku na takin zamani ga kowace karamar hukuma, inda kowace tirela ke É—auke da buhu 600. Wannan na nufin an tanadi jimillar buhu 79,200 domin amfanin manoma a fadin jihar.

“Wannan rabon takin wani bangare ne na shirye-shiryen gwamnati na tallafawa harkar noma a bana, domin Æ™arfafa manoma da tabbatar da wadataccen abinci a jihar,” in ji sanarwar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here