Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan Ta Sake Gurfana a Kotu

0
27

Sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, da aka dakatar, Natasha Akpoti-Uduaghan, ta sake bayyana a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja a ranar Litinin, domin gurfanar da ita karo na biyu kan zargin bata suna ga Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, da tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello.

Akpoti-Uduaghan ta iso kotu tare da mijinta, Emmanuel Uduaghan, da mai rajin kare hakkin dan Adam, Aisha Yesufu; da kuma dimbin magoya bayanta.

Ana sa ran shari’ar za ta gudana ne a gaban Mai shari’a Mohammed Umar.

A ranar 19 ga Yuni, 2025, an fara gurfanar da Sanatar a gaban Babbar Kotun Birnin Tarayya kan irin wadannan tuhuma.

A zaman kotu na baya, alkalin kotun ya ki amincewa da bukatar gwamnatin tarayya na bayar da sammacin kama ta, saboda rashin halartar ta kotu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here