Gwamnatin tarayya ta aike da tawagar ta zuwa jana’izar Dantata a Madina

0
22

Wata tawaga daga Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta isa birnin Madina da ke ƙasar Saudiyya domin halartar jana’izar fitaccen ɗan kasuwa kuma dattijo marigayi Alhaji Aminu Alhassan Dantata.

Alhaji Aminu Dantata ya rasu ne a ranar Asabar a birnin Abu Dhabi, babban birnin Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), yana da shekara 94 a duniya.

Tawagar ta bar Najeriya da yammacin ranar Lahadi, inda ta isa birnin Madina da safiyar Litinin domin halartar jana’izar mamacin.

Jagoran tawagar shi ne Ministan Tsaro na Najeriya kuma tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Muhammad Badaru Abubakar. Tare da shi akwai Ministan Shari’a kuma Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya, Lateef Fagbemi (SAN), Ministan Yaɗa Labarai, Alhaji Mohammed Idris, da Ƙaramin Ministan Gidaje da Raya Birane, Hon. Yusuf Abdullahi Ata.

Haka zalika, manyan malamai da suka haɗa da Sheikh Aminu Daurawa, Dr. Bashir Aliyu Umar da Khalifa Abdullahi Muhammad su ma na cikin tawagar.

Jana’izar marigayi Dantata na ɗaya daga cikin manyan abubuwan da suka ja hankalin al’umma duba da irin gagarumar gudunmawar da ya bayar wajen bunƙasa tattalin arzikin Najeriya da kuma kyautata jin daɗin al’umma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here