Mun yi farin ciki da karyewar farashin wake—Manoma

0
41

Ƙungiyar Manoman Wake, C&BFPMAN, ta bayyana cewa yawaitar amfanin da suka samu a bana na daga cikin manyan dalilan da suka haddasa saukar farashin wake a kasuwannin cikin ƙasar nan.

Shugaban ƙungiyar, Kabir Shuaibu, ne ya bayyana hakan a tattaunawarsa da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), inda ya ce suna murna da yadda farashin wake ya sauka kwanan nan.

A cewar rahoton NAN, daga ƙarshen watanni ukun ƙarshe na shekarar 2024, farashin babban buhun wake mai nauyin kilo 100 ya kai tsakanin Naira 210,000 zuwa Naira 240,000 — sabanin Naira 90,000 da ake sayarwa a shekarar 2023.

Sai dai daga farkon watanni ukun farko na shekarar 2025 zuwa yanzu, farashin ya sauka matuƙa, inda buhu ɗaya ke tsakanin Naira 80,000 zuwa Naira 120,000, gwargwadon nau’in waken.

“Muna farin ciki da wannan sauƙin farashi. Mun samu ninki goma na abin da muke samu a shekarun baya,” in ji Kabir Shuaibu.


LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here