Bani da niyyar ficewa daga jam’iyyar PDP—Gwamnan Enugu

0
25

Gwamnan jihar Enugu, Peter Mbah, ya bayyana cewa ba shi da wani shiri na ficewa daga jam’iyyar PDP.

Mbah ya bayyana hakan ne a ranar Asabar yayin wata ganawa ta musayar ra’ayi da ya yi da mambobin Kungiyar Editocin Najeriya (NGE) a birnin Enugu.

“Har yanzu ina cikin jam’iyyar PDP, kamar yadda kuke ganin, tutar PDP ce ke bayyana a wannan waje,” in ji shi.

Ya amince cewa jam’iyyar na fuskantar wasu ƙalubale na cikin gida, amma ya jaddada cewa irin wannan rikici ba wai ga PDP kaɗai ya ta’allaka ba.

“Duk sauran jam’iyyun siyasa a ƙasar nan suna fuskantar ƙalubale iri daban-daban,” in ji shi.

Gwamnan ya nuna kwarin gwiwa cewa PDP za ta shawo kan matsalolinta a cikin kankanin lokaci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here