Magidanci ya kashe matarsa da adda a jihar Yobe

0
37

Rundunar ‘yan sandan jihar Yobe ta tabbatar da cewa wani mutum mai shekaru 55 mai suna Hamidu Ali ya kai wa matarsa mai shekaru 40 hari da adda, inda ya kashe ta a kauyen Babangida da ke karamar hukumar Tarmuwa.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, Dungus Abdulkarim, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar, inda ya ce lamarin ya faru da safiyar ranar Juma’a.

“A ranar 28 ga Yuni, 2025, da misalin karfe 11 na safe, rundunar ‘yan sanda ta karamar hukumar Tarmuwa ta samu kiran gaggawa daga mazauna kauyen Koriyel, Babangida, Tarmuwa, inda aka sanar da cewa Hamidu Ali, mai shekaru 55, ya kai wa matarsa mai shekaru 40 hari da adda ya kashe ta, wanda ba’a san dalilinsa ba, sannan ya tsere,” inji sanarwar.

Abdulkarim ya kara da cewa jami’an ‘yan sanda na ci gaba da neman wanda ake zargi da aikata kisan.

A wani lamari mai kama da haka, rundunar ta ce ta kama wasu mutane biyu da ake zargi da kashe wani mutum bisa zargin satar waya a karamar hukumar Fika.

Da yake mayar da martani kan wadannan lamurra, Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Yobe, Emmanuel Ado, ya bukaci al’ummar jihar da su guji daukar doka a hannunsu, tare da mutunta doka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here