Hukumomin Saudiyya Sun Amince a Binne Aminu Dantata a Madina

0
22

Gwamnatin Saudiyya ta amince da binne fitaccen ɗan kasuwar Najeriya, Alhaji Aminu Dantata, a birnin Madina mai tsarki.

Sakataren Marigayin na Musamman Mustapha Junaid, ne ya tabbatar da hakan ta wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

A cewar sa, za a kawo gawar marigayin daga Abu Dhabi zuwa Masarautar Saudiyya domin gudanar da jana’iza.

An shirya gudanar da jana’izarsa da safiyar Litinin a birnin Madina.

Alhaji Aminu Dantata, ɗaya daga cikin shahararrun ‘yan kasuwa a Najeriya, ya rasu a birnin Dubai bayan doguwar jinya yana da shekaru 94.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here