Ganduje yayi murabus daga shugabancin jam’iyyar APC na ƙasa

0
27

Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya ajiye mukaminsa nan take.

Ganduje, wanda ya yi gwamna a jihar Kano daga shekarar 2015 zuwa 2023, ya bayyana dalilan lafiyarsa a matsayin abin da ya tilasta masa yin murabus. A cikin wasiƙar da ya rubuta, Ganduje ya ce yana bukatar mai da hankali kan lafiyarsa da walwalarsa.

Sai dai rahotanni daga cikin jam’iyyar na nuna cewa ba batun lafiyar kadai ba ne ya sa Ganduje ya sauka daga kujerar shugabanci.

Tashin-tashinar siyasa da ke ƙara ƙamari a cikin jam’iyyar APC da kuma rashin jin daɗin wasu jiga-jigan jam’iyyar na iya zama wani muhimmin dalili da ya sanya ya yanke wannan shawarar.

Zamanin Ganduje a matsayin shugaban jam’iyyar APC na ƙasa wanda ya fara ne a watan Agustan 2023, ya kasance cike da ƙalubale, ciki har da rikice-rikicen ɓangaranci da matsalolin shugabanci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here