Gwamnan jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule, ya karyata zargin da ke cewa wasu mahara da ke kai hari a jihar Benue na tserewa zuwa Nasarawa domin samun mafaka.
Jihar Nasarawa da Benue na makwabtaka da juna, abin da ya sa ake zargin cewa maharan da ke addabar wasu sassan Benue, musamman yankin Yelwata, sukan tsere zuwa Nasarawa bayan kai hare-hare domin su ɓuya har rikici ya lafa, sannan su dawo su sake kai farmaki.
A kwanakin baya, an yi kisan gilla a garin Yelwata da ke jihar Benue wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da dama, lamarin da ya ƙara tsananta zargin tserewar maharan zuwa Nasarawa.
Sai dai a wata tattaunawa da ya yi da tashar Channels TV a shirin Politics Today a daren Alhamis, Gwamna Sule ya musanta zargin.
Yace jihar Nasarawa tana da nata matsaloli, me zai sa mu zama mafakar mahara.
Mu kanmu muna fama da matsalolinmu na cikin gida, ba mu da dalilin ɗaukar matsalolin wasu, maƙiyaya ma ba su da yawa a Nasarawa,” in ji Gwamnan.
Ya ƙara da cewa tun bayan da ya hau kujerar mulki a shekarar 2019, ya fuskanci ire-iren wadannan zarge-zarge, inda ya bayyana cewa an samu rashin jituwa tsakanin tsohon gwamnan Nasarawa da tsohon gwamnan Benue, Samuel Ortom, har ma ba sa magana da juna.
“Da na hau mulki, na nemi Gwamna Ortom muka zauna, ya kawo korafinsa, na kuma tabbatar masa cewa za mu yi aiki tare don shawo kan matsalar tsaro da ke tsakanin jihohinmu,” in ji Sule.