Fubara na shirin yin sulhu da yan majalisar dokokin Rivers da aka dakatar

0
22

Dakataccen Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara, ya gana da Shugaban Majalisar Dokokin Jihar da aka dakatar, Martins Amaewhule, da wasu daga cikin ‘yan majalisar da ke rikici da shi, inda ake sa ran hakan zai zama dalilin samun sulhu tsakanin su.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa ganawar ta gudana ne a daren Alhamis a birnin Abuja, alamar farko ta kokarin zaman lafiya tsakanin Fubara da ‘yan majalisar da ke cikin rikicin siyasa da shi.

Wadanda suka san yadda taron ya gudana sun bayyana cewa an kammala ganawar cikin nishadi, inda aka hango Fubara da Amaewhule suna dariya tare da rungumar juna.

Majiyoyi sun ce wannan ganawa a Abuja na matsayin matakin farko ne, inda ake sa ran za a gudanar da wata babbar ganawa a gaba, domin tattauna cikakken shirin sulhu.

An dakatar da Gwamna Fubara ne a ranar 19 ga Maris, bayan da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar-ta-baci a jihar saboda tabarbarewar lamuran siyasa. Majalisar Tarayya ta amince da matakin domin dakile rikicin da ke kara kamari a jihar.

Domin daidaita lamarin, Shugaba Tinubu ya nada tsohon Shugaban Hafsoshin Sojin Ruwa, Vice-Admiral Ibok Ete-Ibas, a matsayin mai rikon mukamin gwamna na wucin gadi na tsawon watanni shida, domin bai wa ‘yan siyasar jihar damar sulhu.

Kodayake Fubara ya taba ganawa da Shugaba Tinubu da kuma tsohon jagoransa na siyasa, Nyesom Wike, ganawar da ta gudana da ‘yan majalisa a ranar Alhamis ita ce aka fi dauka a matsayin sahihin matakin warware rikicin gaba ɗaya.

Wike dai ya sha nanata cewa babu batun sasanci na gaskiya sai an fara da sulhu da muhimman masu ruwa da tsaki, musamman ‘yan majalisar dokoki, wadanda aka ce ba a biyansu albashi da alawus na tsawon fiye da shekaru biyu ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here