Kabilar Mumuye tayi watsi da shirin cire mataimakin gwamnan Taraba daga muƙamin sa 

0
21

Matasa ƴan asalin kabilar Mumuye a ƙarƙashin ƙungiyar Mumuye (MCDAYW) sun bayyana rashin amincewarsu da jita-jitar da ke yawo cewa ana shirin sauya Mataimakin Gwamnan Jihar Taraba, Alhaji Aminu Alkali, ba tare da adalci ko tuntuba. 

Matasan sun yi gargaɗin cewa hakan na iya haifar da mummunan tasiri a harkar siyasar jihar.

A cikin wata sanarwa da shugaban ƙungiyar, Ezekiel H. Augustine da sakataren sa Wilfred William Vilaana suka sanya wa hannu, matasan sun bayyana wannan mataki da ake ƙullawa a asirce a matsayin cin zarafi.

Sun nuna cikakken goyon bayansu ga wata sanarwa da babban reshen ƙungiyar MCDA ta fitar a baya, wacce ta yi tir da yunkurin maida kabilar Mumuye saniyar ware a siyasar Taraba.

Sun jaddada cewa idan akwai buƙatar sauya Alhaji Aminu Alkali saboda dalilan rashin lafiya to wajibi ne wanda za a maye gurbinsa dashi ya fito daga ƙabilar Mumuye.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here