Ministan Harkokin Kuɗi na Isra’ila ya bayyana hukuma cewa, kudaden da aka kashe wajen kai farmaki kan Iran sun kai dala biliyan 5.4, yayin da asarar da harin makamai masu linzami ya jawo ta kai dala biliyan 1.35.
Wannan adadi dai shi ne wanda gwamnatin ƙasar ta fitar a hukumance.
Sai dai akwai alamun cewa adadin da ba a bayyana ba ya fi haka yawa, bayan da aka sanar da tsagaita wutar yaki tsakanin Isra’ila da Iran a yaƙin da suka shafe kwanaki 12 ana gwabzawa.