Zan dena goyon bayan Tinubu, in ya ajiye Kashim Shettima—Sheikh Jingir

0
18

Shugaban Majalisar Malamai na Ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bid’a Wa’ikamatis Sunnah (JIBWIS), reshen Jos Sheikh Sani Yahaya Jingir, ya bayyana cewa zai janye goyon bayansa ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu idan har ya cire Kashim Shettima, daga tikitin takara na 2027, kamar yadda rahoton Daily Trust ya bayyana.

Sheikh Jingir ya yi wannan furuci ne yayin wani taron addini da aka gudanar a Masallacin Yantaya da ke Jos, Jihar Filato.

Malamin addinin Musuluncin wanda ya fito fili ya nuna goyon bayansa ga Tinubu a zaben 2023 tare da ƙarfafa mabiyan sa su marawa shugaban ƙasar baya, ya nuna damuwa kan abin da ya kira makirce-makirce na cikin gida don tarwatsa haɗin gwiwar Tinubu da Shettima.

“Ina da labarin cewa wasu marasa kishin ƙasa daga cikin jam’iyyar APC da ma wajenta na kokarin rushe dangantakar Tinubu da Shettima don cimma wasu boyayyun manufofinsu, wanda ba abin alfahari bane, in ji Jingir.

Ya jaddada cewa goyon bayansa ga tikitin Tinubu da Shettima gaskiya ce ta zuciya ba tare da wata manufa ta amfana ba, duk da kasancewarsa na da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar.

A ƙarshe, Sheikh Jingir ya bukaci Shugaba Tinubu da ya yi watsi da masu neman a cire Shettima, yana kiran su da makiyan cigaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here