Wata mummunan fashewar bama-bamai da ta faru a yau Laraba a kan hanyar Maiduguri zuwa Damboa, Jihar Borno, ta yi sanadin mutuwar matafiya hudu tare da jikkatar wasu goma.
Fashewar ta faru ne da misalin ƙarfe 3:30 na rana a kauyen Komala, lokacin da wata motar Suzuki pick-up ta taka Bom din da aka binne a gefen hanya.
Rundunar ‘yan sandan Jihar Borno ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta bayyana cewa an garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa Asibitin Kwararru na Jihar da ke Maiduguri domin kula da lafiyarsu.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda ta jihar, ASP Nahum Daso, ya ce, mutum hudu sun rasu, sannan wasu goma sun samu raunuka iri-iri.”
Fashewar ta haddasa cunkoso mai tsanani a hanyar, lamarin da ya bar matafiya cikin jinkiri na tsawon sa’o’i.
Wannan hari na baya-bayan nan na nuna ci gaba da barazanar da ke tattare da hanyar Maiduguri-Damboa, wadda ta sha fama da irin wannan tashin hankali a baya.
A kimanin watanni biyu da suka gabata, irin wannan hari ya kashe mutum takwas tare da jikkata goma sha ɗaya a yankin.
Hukumomin tsaro sun fara bincike kan wannan lamari, wanda ake zargin cewa mayakan Boko Haram ne ke da hannu a ciki.