Zamu cigaba da kare yancin yan jarida, da walwalar su—Gwamnatin Kano

0
13

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya sake bayyana cikakken kudurin gwamnatinsa na kare ‘yancin ‘yan jarida da kuma inganta ayyukan kafafen yada labarai a fadin jihar.

Wannan jawabi ya fito ne daga Kwamishinan Yada Labarai da Harkokin Cikin Gida, Ibrahim Abdullahi Waiya, yayin bikin rantsar da sabbin shugabannin kungiyar ‘yan jarida ta kasa (NUJ), reshen wakilan kafafen yada labarai na Kano.

A wajen bikin, Kwamishina Waiya ya bayyana shirye-shiryen gwamnatin jihar na tallafa wa ci gaban ƙwarewar ‘yan jarida da horar da su ta hanyoyi daban-daban da za su habaka aikin jarida a Kano da ma wajenta.

Ba da jimawa ba, Ma’aikatar mu zata kaddamar da wasu muhimman tsare-tsare masu tarihi da za su kawo sauyi mai kyau ga ‘yan jarida da kuma harkar jarida baki ɗaya a Jihar Kano, inji Waiya.

Yayin da yake taya sabbin shugabannin murna, Waiya ya bayyana nasarar da suka samu a matsayin shaida ta yadda abokan aikinsu suka amince da su. Haka kuma, ya yaba wa shugabannin baya bisa jajircewa da gagarumar gudummawar da suka bayar.

A jawabinsa na farko, sabon shugaban kungiyar Murtala Adewale, ya sha alwashin jagoranci cikin gaskiya, samar da hadin kai da kuma jin dadin mambobi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here