Gwamnan Kano ya bayar da umurnin gyara kwalejin koyon harsuna Faransanci da yaren China

0
18
Abba Gida-Gida
Abba Gida-Gida

Gwamnan Kano ya bayar da umurnin gyara kwalejin koyon harsuna Faransanci da yaren China

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bayar da umarnin gaggawa akan gyara Kwalejin Koyon Harsunan Faransanci da China da ke ƙarƙashin mallakar gwamnatin jihar.

Bayanin hakan na cikin wata sanarwar da Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida, Kwamared Abdullahi Waiya, ya fitar.

Gwamnan ya bayar da wannan umarni ne yayin wata ziyara ta bazata da ya kai kwalejin da ke garin Kwankwaso, cikin ƙaramar hukumar Madobi.

Yayin ziyarar, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa ya zo domin duba yanayin ginin makarantar da manufar gyara shi don jin daɗin ɗalibai da malamai. 

Ya kuma nuna jin daɗinsa matuƙa kan hazakar ɗalibai da malamai, musamman yadda ɗaliban ke iya jin harsunan ƙasar China da Faransanci.

 “Na gamsu da yadda ɗaliban ke fahimtar karatu, musamman yadda suke iya harsunan amma kuma na damu ƙwarai da halin da gine-ginen makarantar ke ciki, inji Abba.

Gwamnan ya bayar da umarni kai tsaye ga Kwamishinan Ayyuka na Jihar Kano akan fara gyaran dukkan gine-gine da sauran sassan makarantar da suka lalace. Ya jaddada cewa gwamnatin jihar za ta fara aikin sabunta dukkan kayan more rayuwa da ke cikin makarantar ba tare da ɓata lokaci ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here