Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya sha alwashin cewa gwamnatinsa ba za ta saurara ba har sai an tabbatar hukunta wadanda suka kashe wasu matasa biyu ‘yan Kano a jihar Benue.
Matasa da aka kashe su ne Barhama Suleiman da Jamilu Ahmad, inda aka kai musu hari har lahira a daren Litinin a birnin Makurdi dake Jihar Benue.
Rahotanni sun bayyana cewa wasu mutane da ba a san ko su wane ba sun far masu da misalin karfe 11:00 na dare, inda suka ci mutuncinsu tare da kashe su cikin zalunci, bisa zargin cewa matasan Fulani ne.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, Gwamna Yusuf ya bayyana harin da cewa “mugun aiki ne da ba shi da dalili kuma abin ƙyama.”
“Zuciyata cike take da baƙin ciki da ɓacin rai wajen sanar da mutuwar waɗannan matasa biyu. Ba su da wani laifi face yin amfani da haƙƙin su na kundin tsarin mulki wajen rayuwa da yin aiki a kowace ɓangare na ƙasar nan,” in ji Gwamna Yusuf.
Yusuf ya jaddada cewa kowane dan Najeriya na da ‘yancin rayuwa a ko’ina cikin ƙasar ba tare da fargaba ko nuna wariya.