‘Yan Majalisa  biyu sun fice daga PDP da LP zuwa APC

0
26

Wasu yan majalisar wakilai guda biyu daga PDP LP sun sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC.

‘Yan majalisar da suka sauya sheƙa su ne, Hon. Peter Akpanke, mai wakiltar mazabun Obanliku/Obudu/Bekwarra a Jihar Cross River.

Sai Farfesa Paul Nnamchi, mai wakiltar mazabun Enugu East/Isi Uzo a Jihar Enugu.

Sun bayyana rikice-rikicen cikin gida a cikin jam’iyyunsu na baya da kuma buƙatar daidaita kansu da manufofi da shirye-shiryen Gwamnatin Tarayya a matsayin dalilan sauya shekar da suka yi.

Da yake karanta wasikun sauya shekar a zaman majalisar, Kakakin Majalisar Wakilai, Hon. Abbas Tajudeen, ya taya su murna bisa matakin da suka dauka na komawa jam’iyyar APC mai mulki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here