Najeriya ta tattara Naira triliyan 6.9 a watanni 3 na farkon 2025 – Ministan Kudi

0
26

Ministan Kudi Wale Edun, ya bayyana cewa Najeriya ta samu kudaden shiga da suka kai naira tiriliyan 6.9 a cikin watanni ukun farko na shekarar 2025.

Edun ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, yayin wani taron tuntuba da wayar da kai tsakanin gwamnati da ‘yan kasa da masu ruwa da tsaki, dangane da aiwatar da manyan manufofin Shugaba Bola Tinubu, wanda aka gudanar a birnin Abuja.

Ministan ya ce wannan adadi ya nuna karin kaso 40 cikin 100 idan aka kwatanta da naira tiriliyan 5.2 da aka samu a daidai wannan lokaci a shekarar da ta gabata.

A cewarsa, tabbatar da gaskiya da bude hanyoyin karbar kudaden shiga da kuma yadda ake tura su cikin asusun gwamnati, ya taimaka matuka wajen kara yawan kudaden da gwamnati ke samu.

Ya kara da cewa karin kudaden ya biyo bayan wasu sauye-sauye da aka samu kwanan nan, musamman wadanda suka shafi musayar kudade.

Edun ya tabbatar da cewa gwamnati na ci gaba da daukar matakan hana zurarewar kudade ta hanyar amfani da fasaha da kirkire-kirkire domin inganta tara kudaden shiga.

Haka kuma, ya bayyana cewa gwamnati na kokarin kara daidaito a harkar kashe kudi, inda ya ce adadin bashin da ake biya idan aka kwatanta da kudaden shiga ya sauka zuwa kashi 60 cikin 100 daga kashi 150 cikin 100 da aka taba samu a baya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here