Wasu bayanai daga majiya mai tushe a birnin Abuja sun nuna cewa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu na iya sauya Mataimakin da Kashim Shettima da Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, a yayin zaben 2027.
Rahotanni daga jaridar BusinessDay, sun bayyana cewa hakan na iya zama daya daga cikin dalilan da suka sa shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, bai nuna goyon baya ga Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima ba a taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC da aka gudanar a Jihar Gombe.
Wata majiya daga cikin jam’iyyar ta bayyana wa BDSunday cewa akwai goyon baya mai ƙarfi daga wasu jiga-jigan jam’iyyar game da zaɓen Kwankwaso, domin tabbatar da samun nasarar sake zaɓen Tinubu a 2027.
Majiyar, wacce ta buƙaci a sakaya sunanta, ta ce ana ci gaba da tattaunawa, sannan ana kokarin shawo kan Kwankwaso ya dawo cikin jam’iyyar APC, kuma ya ziyarci Shugaban Ƙasa kwanan nan.
Majiyar tace Kwankwaso yana da abubuwan da Shugaban Ƙasa da jam’iyyar APC ke buƙata domin samun nasara a 2027.
Har ila yau, majiyar ta bayyana cewa ana kallon Kwankwaso a matsayin babban jari ga jam’iyyar, sakamakon ƙwarewarsa da kuma ɗumbin masoyansa musamman a Arewacin ƙasar nan ta hanyar ƙungiyar Kwankwasiyya.