Shugaba Tinubu yayi ala wadai da harin Konduga, da jajen fashewar Bom a Kano

0
23

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi Allah wadai da harin kunar bakin wake da ya afku a garin Konduga, Jihar Borno, a ƙarshen mako, inda shugaban ya bayyana harin a matsayin aikin da ya nuna ƙarancin imani da tsoro.

A cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Lahadi, shugaban ƙasar ya bayyana matuƙar damuwa da ɓacin rai kan wannan hari tare da mika ta’aziyyarsa ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu.

Shugaban ƙasa ya yi kira ga hukumomin tsaro da su ƙara ƙaimi wajen kawar da sauran ‘yan tada kayar baya na Boko Haram da suka koma kai hare-hare a wuraren da ba a tsaurara tsaro ba, domin karkatar da hankali.

Haka kuma, Shugaba Tinubu ya yi ta’aziyya ga gwamnatin Jihar Borno da al’ummarta, tare da umartar Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) da ta kai ɗauki ga waɗanda suka tsira daga harin.

A wani cigaban, shugaba Tinubu ya bayyana alhininsa kan fashewar da ta faru a wata masana’antar sarrafa ƙarafa a Jihar Kano, wanda ya shafi mutane 15, inda biyar daga cikinsu suka rasa rayukansu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here